Yadda ta fara kasance a shirin gurfanar da waɗanda ake zargi da kisan matar aure da ‘ya’yanta a dorayi Kano

IMG 164854 11326 1773244144187

Gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba ta gabatar da takardun tuhuma gaban kotun majistiri dake No-man’s-land kan matasa 3 da ake zargi da kisan matar aure da ‘ya’yanta 6 a unguwar Dorayi Chiranchi a jihar Kano

Babban sakatare a ma’aikatar shari’a, Barrister Salisu Muhammad Tahir, ya bayyana wa kotu cewa gwamnati ta kammala bincike tare da rubuta takardar tuhuma kan wasu matasa da ake zargi da aikata laifukan domin gurfanar da su a gaban kotu mai hurumi.

Ya ce daga cikin mutanen da aka gurfanar akwai mutum guda da aka wanke daga zargin kisan kai, sai dai ana tuhumar sa da hannu a wani lamari da ya shafi zargin yi wa wata yarinya fyade, wacce daga bisani ta rasu bayan an zarge su da kwakwule mata idanu.

An gurfanar da Umar Auwal, Yakubu Dayyabau, Isyaku Yakubu da kuma Umar Ali a gaban kotu bisa zargin haɗa baki da aikata kisan kai a unguwar Dorayi.

Takardar tuhumar ta nuna cewa matasan sun haɗa baki wajen kashe wasu mutane a unguwanni daban-daban, bisa zargin aikata tsafi.

Daga cikin mutanen da ake zargin sun kashe akwai wata mata tare da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi, da kuma wata mata tare da abokiyar zamanta a unguwar Tudun Yola. Haka kuma akwai wata ƙaramar yarinya da ake zargin an yi mata fyade kafin daga bisani aka kashe ta.

Lauyoyin gwamnati sun shaida wa kotu cewa an riga an kammala rubuta tuhume-tuhumen domin gurfanar da matasan a gaban babbar kotun jiha domin ci gaba da shari’ar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *