Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira da a hada karfi da karfe tsakanin manyan masu rike da mukaman gwamnati a kowane mataki da kuma abokan huldar ci gaba a yunkurin da ake na fatattakar ‘yan Najeriya daga kangin talauci da inganta rayuwar ‘yan kasa baki daya.
Alfijir Labarai ta rawaito mataimakin shugaban kasar yace hakan ba zai taba faruwa ba idan duk masu hannu a harkar mulki ba su hada kai da juna ba don samar da yanayin da kowane dan Najeriya zai samu damar ci gaba.
Shettima, wanda ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin taron majalisar tattalin arzikin kasa karo na 144 da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, ya bayar da shawarar hanyoyin da za a bi wajen magance bukatun ‘yan kasa cikin gaggawa, ciki har da gina tsare-tsare masu dorewa da zai ba su damar dogaro da kai. da wadata.
Sai dai ya yarda cewa duk da cewa matsalolin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gada ba za a iya magance su cikin dare daya ba, duk da dadewar da ake samu na magance matsalolin da ake fama da su, amma ‘yan Najeriya na bukatar daukar matakan gaggawa, masu tasiri.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj