‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 37 Bisa Zargin kashe Iyayensa

Alfijr ta rawaito Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Alhamis.

Alfijr Labarai

Shiisu ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan da ya kai wa mahaifinsa da mahaifiyarsa da wasu mutane biyu hari da wani katako.

Wadanda ake zargin sun kai wa harin sun hada da, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, Hauwau Ahamadu mai shekaru 60, Kailu Badugu mai shekaru 65 da kuma Hakalima Amadu mai shekaru 60.

Shiisu ya ce, tawagar ‘yan sanda ta kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Gumel, inda Ahmadu Muhammad da Hauwau Ahmadu suke.

likitoci sun tabbatar da sun mutu sakamakon raunukan da suka samu a harin.

Alfijr Labarai

Kakakin ya kara da cewar, sauran biyun da abin ya shafa an kan kwantar da su a asibiti domin yi musu magani.

“Yau da misalin karfe 11:30 na safe ne muka samu labarin cewa wani Munkaila Ahmadu da ke kauyen Zarada-Sabuwa a karamar hukumar Gagarawa ta Jihar Jigawa, ya yi amfani da wani katako ya far wa wadannan mutane: “Ahmadu Muhammad, Hakimin Zarada-Sabuwa. Hauwa Ahmadu, Kailu Badugu da Hakalima Amadu, dukkansu a kauyen Zarada -Sabuwa a karamar hukumar Gagarawa.”

Ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda suka mutun iyayen wadanda ake zargin ne.

Alfijr Labarai

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Tafida, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin, inda daga nan ne za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

(NAN)

Slide Up
x