Yan Sanda Sun Kama Ma’aikacin Kotu Kan Zargin Wawure Milyan 35, Na Marayu

FB IMG 1766328120482

‘Yan sanda sun cafke Sadiq Sani Sadiq, magatakarda mai kula da harkokin kudi na Babbar Kotun Shari’a dake Goron Dutse a Jihar kano, domin ci gaba da fadada bincike akan zargin da ake yi masa da karkatar da naira milyan 35, kudin rabon gadon wasu marayu tara da aka ba shi ajiya.

A makon da ya gabata ne Daraktan Yada Labarai da Kididdiga na Kotun Daukaka Karar Shari’a dake Kano, Muzammil Ado Fagge ya bayyana wa Justice Watch Hausa, cewar zai yi bincike akan zargin da ake yi wa Magatakarda Kotun.

Bayan da Justice Watch Hausa ta sake tuntubar Muzammil yau, ya tabbatar da cewar, a halin da ake ciki yanzu, tuni Yan’sanda suka kame Sadiq domin gudanar da bincike akan zargin da ake yi masa.

A baya dai Fagge ya tabbatar da cewar idan har abin da ake zargi akan magatakardan Kotun ya zama gaskiya to hakika hakan babban keta doka ne a tsarin Shari,a.

Ya Kuma tabbatar da cewar sabon tsarin da Shugaban Alkalan Kotunan Shari’ar Musulunchi Khadi Tijjani Yusuf Yakasai ya samar, ya haramta ajiye kudin gado a asusun kowanne ma’aikaci sai dai na gwamnati.

Abba Inuwa, daya daga cikin iyalan mamacin da suka shigar da kara a gaban babbar kotun shari’a dake Goron Dutse domin raba musu gadon mahaifinsu yace, bayan an siyar da rumfar kasuwa ta mahaifinsu da ta rage, a cikin asusun Sadiq Sani Sadiq, maimakon asusun Gwamnati, sai suka shiga wasan buya da shi.

A wata majiya daga ma’aikatar Shari’a da ta nemi da a boye sunanta ta tabbatarwa da Jaridar Justice Watch Hausa cewar kudaden marayu da ake nema a hannun Sadiq a yanzu haka sun kai milyan hamsin.

“Akwai korafe korafe na karkatar da kudin marayu masu yawa akan sa.” In ji majiyarmu.

Ko baya ma Justice Watch ta ruwaito cewar an taba gurfanar da wasu maaikatan Kotunan Shari’ar, wadanda suka hadar da Alkalai masu aiki da wadanda su ka yi ritaya, inda aka yi zargin sun hada kai da wasu maaikata a Hukumar Yan Fansho ta Jihar Kano  suka wawure sama da Naira Milyan Dari biyar daga asusun Gwamnatin Kano.

Majiyarmu ta ce daga baya an wanke wasu da ake zargi soso da sabulu daga zargin da ake yi musu.

Karanta Labari: Babbar Kotun Kano Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Biyu da Aka Samu da Laifin Kisan Kafinta

A halin da ake ciki yanzu, iyalan mamacin, sun roki Babbar Jojin Kano, Mai Shari’a Dije Aboki, da Shugaban Alkalan Kotunan Shari’ar dake Kano da Hukumar JSC da su taimaka musu.

A yanzu haka dai Al’umma sun kasa kunne suna sauraren sakamakon bincike da za fitar akan zargin da ake yi wa Magatakarda Kotun Sadiq Sani Sadiq.

Justice watch

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *