Yanzu-yanzu: An Rantsar Da Bassirou Faye a matsayin shugaban kasa mafi karancin shekaru a Afirka

IMG 20240402 WA0031

Daga AAminu Bala Madobi

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban kasa mafi karancin shekaru a Senegal da Afirka bayan ya samu nasara a zagayen farko kan alkawarin kawo sauyi kwanaki 10 bayan an sako shi daga gidan yari.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban mai shekaru 44 da haifuwa ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Talata a wata cibiyar baje koli da ke sabon garin Diamniadio kusa da Dakar babban birnin kasar.

“Ina Mai rantsuwa da Allah gaban al’ummar Senegal, na yi rantsuwa kama aiki amatsayina na shugaban Jamhuriyar Senegal,” in ji shi.

An gudanar da bikin ne a gaban wasu shugabannin Afirka da suka hada da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya.

Daga nan ne za a mika mulki a hukumance tare da shugaba Macky Sall a fadar shugaban kasa da ke Dakar.

Faye na daya daga cikin gungun ‘yan adawar siyasa da aka sako daga gidan yari kwanaki 10 kafin zaben shugaban kasa na ranar 24 ga Maris a karkashin afuwar da Sall ya sanar wanda ya yi kokarin jinkirta zaben.

An kaddamar da yakin neman zaben Faye ne yayin da yake tsare a gidan yari.

Tsohon mai binciken harajin zai zama shugaban kasar Afirka ta Yamma na biyar tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

A yayin da yake aiki tare da mai gidan shi Ousmane Sonko, wanda aka hana shi shiga zaben, Faye ya bayyana abubuwan da zaisa a gaba a cikin jawabinsa na nasara: sulhunta kasa da kasa, sauƙaƙa tsadar rayuwa da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Shugaban ya sha alwashin maido da ikon kasa kan muhimman kadarori kamar su bangaren mai, iskar gas da kamun kifi.

A bangaren kasa da kasa, Faye na neman dawo da kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da ke karkashin mulkin a cikin kungiyar ECOWAS.

Wanda aka fi sani da Diomaye, ko kuma “mai daraja” a yaren Serer na gida, ya lashe zaben ranar 24 ga Maris da kashi 54.3 na kuri’un.

Faye, musulmine da ya fito daga cikin iyalai sanannu, yana da mata biyu da ’ya’ya hudu.

Sai dai Faye ba shi da rinjaye a Majalisar Dokoki ta kasa, kuma zai nemi kulla kawance don samar da sabbin dokoki, ko kuma kiran zaben ‘yan majalisa na tsakiyar watan Nuwamba.

Babban kalubalen shi ne samar da isassun ayyukan yi a kasar da kashi 75% na al’ummar miliyan 18 ke da shekaru kasa da 35 kuma yawan marasa aikin yi a hukumance ya kai kashi 20%.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *