Yanzu-Yanzu! Gwamnatin Najeriya Ta Garkame Kantin Sahad Store

FB IMG 1708081738586

Gwamnatin Tarayya ta garkame kantin SAHAD STORE da ke ABUJA, sakamakon zargin kara kudin kaya babu gaira babu dalili.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar kare hakkin masu sayan kaya ta kasa (Federal Consumer Protection Council), ce ta dauki wannan mataki da safiyar juma’a.

Rahotanni sun ce, kantin na Sahad Store da ke Abuja, yana karbar kudin kayan da abokan huldarsa suka saya da ya sha banbam da abin da aka rubuta a matsayin kudin kayan da ke ajiye a kanta; ma’ana idan aka rubuta Naira 100 a jikin kaya, in kaje biyan kudi sai ace Naira 200 ne.

A jiya alhamis ne shugaban kasa Bola Ahmed TINUBU ya shaidawa gwamnonin Nigeria cewa, ‘yan-sanda, jami an hukumar tsaro ta DSS da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki na gwamnatin tarayya, za su fara bi lungu da sako na kasar nan domin zakulo inda ‘yan kasuwa suka boye kayayyakin abinci domin jira yayi tsada.

FB IMG 1708081742400
📸 Federal

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

One Reply to “Yanzu-Yanzu! Gwamnatin Najeriya Ta Garkame Kantin Sahad Store”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *