Daga Aminu Bala Madobi
Shugaba Donald Trump a ranar Talata ya yi fatali da rade-radin da ake na kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi a shekarar 2018, yana mai cewa dan jaridan mai adawa da kasar Saudiyya yana da matukar haÉ—ari.
A wata ganawa yayin ziyarar aiki Trump yace yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman zai kunyata masu kokarin shafa masa kashin kaji.
Trump ya dage cewa Yarima bin Salman – wanda hukumar leken asiri CIA ta kiyasta cewa mai yiwuwa ne ya ba da umarnin kisan – ko da ba shi da hannu a ciki.
“Bai san komai ba game da shi ba, kuma za mu iya barin shi a haka. Ba dole ba ne ka kunyata baÆ™onmu ta hanyar yin tambaya irin wannan ba,” in ji Trump.
Ya kara da cewa Saudi Arabiya ta bi duk matakan da suka dace na bincike kuma “muna yin iya kokarinmu don kada hakan ya sake faruwa.”
Yau Talata ne Yariman ya kai ziyara Birnin Washington na farko tun a shekarar 2018, watanni kafin kisan Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya.
Kididdigar da hukumar leken asiri CIA ta fitar a shekarar 2021 ta gano cewa yariman ya amince da kashe mawallafin jaridar Washington Post, saidai kuma ya dade ya na musantawa
Me Zaku Ce?
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t