Zaɓe: Hukumomi sun katse intanet a Kamaru

FB IMG 1761248371112

Rahotanni na cewa an samu katsewar intanet a sassa da dama na kamaru, yayin da ‘yan ƙasar ke ci gaba da jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi kusan mako biyu da suka wuce.

Wata ƙungiya mai sanya ido kan harkokin Intanet mai suna NetBlocks ta ce katsewar intanet din ta shafi har wasu ƙasashe makwaftan Kamaru.

Masu amfani da intanet sun ce sun samu sako daga kamfanonin sadarwa cewa katsewar ta wucin gadi ce.

Katsewar intanet din na zuwa ne a yayin zaman ɗarɗar ke ƙaruwa a kasar, inda ƙungiyoyin ‘yan’adawa ke kiran a ci gaba da gudanar da zanga-zanga idan har majalisar kundin tsarin mulkin kasar ta bayyana abin da suka kira sakamakon ƙarya.

Hukumomi sun haramta duk wani taro, da zirga-zirgar babura da tasi a birane da dama, yayin da ake jiran sakamakon zaben a ranar Litinin mai zuwa.

BBC

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *