Zargin cin zarafi: BBC ta ki karbar takardar ajiye aikin shugaban sashin Hausa

FB IMG 1756461452157

Gidan Radio BBC, ya dakatar da Editan Sashen Hausa, Aliyu Tanko, na tsawon watanni uku bisa zargin cin zarafi da tsohuwar ma’aikaciyar gidan, Halima Umar Saleh, ta yi masa.

Haka kuma an kafa wani kwamiti na bincike kan ƙorafe-ƙorafe da dama da wasu tsoffin ma’aikata da kuma waɗanda har yanzu ke aiki a BBC Hausa suka shigar kan Tanko.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa mataimakin shugaban BBC News kuma daraktan BBC News Global, Jonathan Munro, ne ya bayar da umarnin gudanar da binciken, tare da aiko da tawaga daga Landan zuwa Abuja domin gudanar da shi.

Majiyar ta ce an shaida wa Tanko cewa ba zai iya yin murabus ba, yayin da aka dakatar da shi tare da gudanar da bincike .

“An ƙi amincewa da murabus ɗin ne bisa dalilin cewa bai bi ƙa’ida ba. A matsayinsa na babban jami’i, wajibi ne ya bayar da sanarwar watanni biyu kafin a amince da murabus ɗinsa, ko kuma ya biya albashin watanni biyu idan ba ya son jira – haka ma idan kamfanin ne zai kawo ƙarshen aikinsa,” in ji majiyar.

Sai dai a wata tattaunawa da Daily Nigerian, Aliyu Tanko ya tabbatar da cewa ya ajiye aikinsa daga BBC.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *