Ziyarar Matar Gwamnan Katsina MAAUN

 ZIYARAR MATAR GWAMNAN JIHAR KASTINA HAJIYA HADIZA BELLO MASARI ZUWA JAMI’AR MARYAM ABACHA AMERICAN NAJERIYA JAHAR KANO. 

A jiya ne 2 ga Disamba, 2021, uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Hadiza Bello Masari tare da ayarin motocinta, suka kai ziyarar ban girma a jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, jihar Kano. 

Shugaban kungiyar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya tarbe su, inda ya jagorance su a rangadin jami’ar domin shaida irin gagarumin aikin da cibiyar wasanni, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, da masallaci, da manyan makarantu da sauran wurare. 

Uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Hadiza Bello Masari, ta bayyana matukar jin dadin ta kan yadda a zahiri ake yin kokari wajen kafa jami’ar, inda ta ce ta dade tana jin abubuwa masu kyau game da jami’ar, shi ya sa tayi kokarin kawo ziyara. 

Ta kuma yi addu’ar Allah ya saka wa al’ummar kasa  kishi irin na Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, tare da fatan jami’ar ta fara ayyuka cikin gaggawa.

 Shugaban MAAUN ya kuma nuna jin dadinsa da wannan ziyara tare da yi musu addu’ar Allah ya dawo da su gida lafiya. 

Daukar Hoto Maaun Press

Ga Vedio Ga masu Sha awar kallo

Best Seller Channel 

Slide Up
x