Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Daya, Sun Debe Mutane 45’ A Kaduna

Alfijr ta rawaito a ranar Kirsimeti wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane 45 a unguwar Angwan Aku da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

An ce harin ya afku ne da safiyar Lahadi a lokacin da mazauna yankin ke shirin zuwa coci domin bikin Kirsimeti.

Wasu ganau sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki a kauyen a kan babura.

“Sun zo ne da misalin karfe 10 na safe ranar Lahadi lokacin da mutane ke shirin zuwa coci,” in ji wani mazaunin unguwar.

“Akwai da yawa kuma sun ajiye baburansu a kan hanyar daji kafin su shiga kauyen, suna harbi lokaci-lokaci.

“Suna bi gida-gida, suna garkuwa da mutane. In Ji shi

Sun kashe mutum daya suka tafi tare da mutum 53, amma mutane bakwai suka tsere suka dawo.

“Don haka, mutane 45 suna tare da su.”

An ce al’ummar na da nisa da Mararaban Kajuru, yankin da wani sansanin sojoji yake.

Mohammed Jalige, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna, ya ce bai da labarin faruwar lamarin har ya zuwa lokacin mika wannan rahoton.

Sai dai ya ce zai bayar da karin bayani idan ya tabbatar da harin.

The Cable
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

2 Replies to “Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Daya, Sun Debe Mutane 45’ A Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *