Jama’a da kungiyoyi ne ke ci gaba da Allah wadai biyo bayan kisan matashiya Mariama Cisse ‘yar shekara ashirin da biyar da ta yi suna a shafukan sada zumuntan na Tik -Tok bayan garkuwa da ita, a garin Tonka a yankin Timbuktu dake ƙasar Mali
Wannan matashiya ta na da akala mutane ko mabiya 95,000 da ke biyarta a shafin Tik-Tok inda ta ke bayyana goyon bayanta ga sojojin Mali.
Kisan da aka yi mata ya haifar da bacin ran jama’a a Mali da wajen ƙasar.
Rahotanni na nuni da cewa wannan matashiya bayan ta isa wata kasuwa da ke daf da yankin,ta kuma ci gaba da yada wani bidiyo kai tsaye daga kasuwar,wasu mutane dauke da makamai suka kama ta da kuma awon gaba da ita kafin daga bisani su dawo da ita washegari zuwa babban filin Tonka na garin inda aka kashe ta a gaban taron jama’a.
Marima Cisse ta kasance tauraruwa a garinsu da ke arewacin Mali. A cikin bidiyonta,a wasu lokuta ta na mai barkwanci ko suka,Mariam Cissé ta kuma nuna goyon bayanta ga sojojin Mali. Ɗaya daga cikin rubuce-rubucenta ya nuna tana sanye da kayan sojoji a lokacin da ta aike da sakon da ya haifar da fushinmasu da’awar jihadi da kuma ke yaki da dakarun Mali.
RFI
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t