Ƙasar China Ta Gargadi Amurka Kan Tsoma Baki Cikin Harkokin Najeriya

FB IMG 1762260773027

Gwamnatin kasar China ta yi gargadi ga Amurka kan duk wani yunkuri na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya, bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na amfani da sojoji don hukunta Najeriya kan zargin cin zarafin Kiristoci.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, Mao Ning, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, ya bayyana cewa Beijing “na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu gaba ɗaya wajen tafiyar da al’amuran Najeriya a kan hanya madaidaiciya da ci gaba.”

Mao ya kara da cewa:”China, a matsayin ta na abokiyar haɗin gwiwa, tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko hujjar kare haƙƙin ɗan adam wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gida, ko yin barazanar takunkumi ko amfani da ƙarfi.”

Wannan martani na China ya biyo bayan damuwar da maganganun Trump suka haifar a fadin Afirka da sauran sassan duniya, inda ƙasashe da dama suka yi Allah wadai da barazanar Amurka.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *