Ƙungiyar Iyayen Daliban MAAUN Sun Jinjinawa Farfesa Gwarzo Bisa Nasarar Bikin Yaye Dalibai

IMG 20260104 WA0657

Ƙungiyar Iyayen Daliban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) ta jinjinawa Shugaban Rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, tare da taya shi murna bisa nasarar kammala shirya bikin yaye daliban jami’ar karo na farko cikin nasara da kwanciyar hankali.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Mustapha Balarabe, ne ya bayyana hakan a madadin daukacin iyayen dalibai yayin wata hira da manema labarai, bayan kammala bikin yaye daliban da ya gudana a harabar jami’ar da ke Kano.

Alhaji Mustapha ya ce abin da ya fi burge su kuma ya sa suka yi wannan yabo shi ne yadda Farfesa Gwarzo ya ɗauki nauyin dalibai 45 da suka kammala karatu da sakamako mafi kyau, inda ya ba su guraben karatun digiri na biyu a jami’o’in ƙasashen waje.

“Wannan abin a yaba wa ne matuƙa, domin ya ƙara mana ƙwarin gwiwa tare da jawo hankalinmu na ƙarfafa sauran iyaye su kawo ’ya’yansu su yi karatu a wannan jami’a mai albarka,” in ji shi.

Ƙungiyar ta kuma yaba da yadda Shugaban Rukunin Jami’o’in ke ci gaba da bunƙasa harkokin koyarwa da inganta ilimi a jami’ar. Ta ce, duk da irin wannan ci gaba, MAAUN na daga cikin jami’o’in masu zaman kansu mafi araha a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, a daidai lokacin da wasu jami’o’i ke karɓar kuɗin karatu naira miliyan shida ko bakwai ga masu karatun aikin jinya (Nursing), MAAUN na karɓar ƙasa da naira miliyan biyu a duk zangon karatu.

Haka zalika, ƙungiyar ta nuna takaicinta kan yadda wasu ’yan tsiraru ke ƙoƙarin bata sunan jami’ar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin takaici ƙwarai.

Alhaji Mustapha ya ce, “MAAUN na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin jami’o’in masu zaman kansu mafi araha a Nijeriya, tare da bayar da ingantaccen ilimi da kyakkyawan tsarin gine-gine. Wasu jami’o’in masu zaman kansu a kasar na karɓar kuɗin karatu har sau uku na MAAUN, amma babu wanda ke tayar da hankali a kansu. To, me ya sa ake nufin MAAUN kaɗai?” ya tambaya.

Ya kuma ƙarfafa gwiwar wanda ya kafa jami’ar da ya ci gaba da tsayawa daram tare da jajircewa wajen bayar da ingantaccen ilimi, yana yaba masa bisa kishin ƙasa da kuma yadda ya ci gaba da daidaita kuɗin karatu duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da suka tilasta wa cibiyoyi da dama ƙara nasu kuɗaɗen karatu.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *