Kalaman Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ke nan kan gwamnan Jihar Kano Abba Kabiru Yusuf a cikin wani sakon taya gwamnan murnar cikarsa shekaru 63, wanda kakakin Tinubun Bayo Onanuga ya fitar.
Tinubu ya ce sauÆ™in kai, Æ™asÆ™antar da kai da kuma jajircewar gwamnan sun bayyana Æ™arara a yadda yake tafiyar da al’muran Jihar Kano.
Ya ci gaba da cewa “Ina da tabbacin ka biyo hangen nesa irin na Malam Aminu Kano a siyasar ci-gaba, da bunÆ™asa ci-gaba tun daga tushe da kuma ceton talakawa.”
Tinubu ya kuma yaba wa Gwamna Abba wajen ayyukan ƙawata birnin da suka hada sabunta birane da gina tituna da gadoji.
Sannan ya jinjina masa wajen ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, abin da a cewarsa ya sa Kano ta samu gagarumar nasara a jarrabawar NECO.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t