Ƴan sanda sun fake da barazanar tsaro ne kawai don su hana Maulidin Tijjaniyya – Gwamnatin Kano

FB IMG 1723959647845

Gwamnatin Jihar Kano ta zargi ƴasanda da kokarin hana taron addini na na dariƙar Tijjaniyya na shekara-shekara a jihar, inda ta ƙaryata cewa akwai barazanar tsaro a jihar kamar yadda rundunar ƴansanda ta sanar a yau a jihar.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a Fadar Sarkin Kano a yau Juma’a, Kwamishinan yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya musanta gargadin da ‘yan sanda suka fitar tun da fari.

Waiya ya ce rundunar ƴansanda kawai ta fake da barazanar tsaro ne don ta hana gudanar da taron Mauludin na Tijjaniyya na kasa, wanda ya ce an kwashe kisan shekaru 40 ana gudanar da shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa, duk da matakin da ƴansanda suka dauka, Mauludin zai gudana  kamar yadda aka tsara a filin wasa na Kofar Mata, yana mai tabbatar wa wadanda ke son halarta cewa gwamnatin jihar ba za ta bari a samu wata matsala ba.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *