Ƴan Sanda sun magantu kan mutuwar jami’in Civil Defense a wajen rabon shinkafa a Kano

FB IMG 1765809781140

Rundunar ’yansandan jihar Kano ta sanar da fara bincike kan mutuwar wani jami’in hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) da ya rasa ransa bayan wasu bata-gari sun kai hari yayin wani  taron tallafawa jama’a a karamar hukumar Tudun Wada.

A cikin wata sanarwar manema labarai da rundunar ta fitar ranar 14 ga Maris, 2026, ta ce lamarin ya faru ne a ranar 13 ga Maris lokacin da wasu bata-gari suka kai hari a wurin taron bada tallafin.

Kwamishinan ’yansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ’yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata laifin tare da cafke su.

Ya tabbatar wa al’umma cewa ba za a bar wani abu a kasa ba wajen tabbatar da an hukunta masu hannu a harin.

Sanarwar ta ce an garzaya da jami’in zuwa Asibitin Kwararru na Tudun Wada, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa, sannan daga bisani aka kai gawarsa asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) domin ajiye ta a dakin ajiye gawa.

Rundunar ’yansandan ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin da kuma hukumar NSCDC, tare da kira ga jama’a da su bai wa jami’an tsaro hadin kai yayin da bincike ke gudana.

Kakakin rundunar ’yansandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanya hannu kan sanarwar a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *