Ƙungiyar IZALA ta tallafawa jahar Borno da shinkafa tirela ɗaya

Izala

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa iƙamatis sunnah ta tarayyar Naijeriya, ta kai ziyarar jaje garin Maiduguri, inda ta ziyararci gidan gwamnatin jahar Borno da fadar Shehu Borno.

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, shi ya jagoranci tafiyar, inda ya jajantawa gwamnan Borno Professor Babagana Umara Zulum ga jarrabawar da ta afkawa jahar na ambaliyar ruwa wanda yasa akayi asarar rayuka da dukiyoyi. Sheikh Bala Lau bai tsaya a jajantawa kawai ba, ya haɗa da tausayawa inda ya bada gudunmawar shinkafa (50KG) tirela ɗaya mai ɗauke da buhu ɗari shida domin a tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.

Kazalika tawagar ta ziyarci fadar mai martaba Shehun Borno Alhaji (Dr) Abubakar Ibn Umar Garbai Al’amin El-kanemi CFR, domin jajantawa, inda shugaba Sheikh Bala Lau yayi wa’azi akan idan Allah ya jarrabi bayinsa da irin wannan, Suyi hakuri har suci wannan jarrabawa.

A maida bayanansa, Gwamnan jahar Borno ‘Frofessor’ Babagana Umara Zulum yayi matuƙar Godiya da wannan ziyarar jajantawa da ƙungiyar Izala ta yi musu, sannan yayi godiya da shinkafa da ƙungiyar ta bada a matsayin gudunmawa, ya kuma yi alƙawarin zai raba shinkafar ga mutane cikin adalci insha Allah.

Kaɗan daga cikin Tawagar da suka rufawa shugaban baya, Akwai shugaban majalisar Malamai Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sheikh Yakubu Musa, Sheikh Kabir Gombe, Engr Mustapha Imam Sitti, Alaramma Ahmad Sulaiman, Alaramma Nasiru Gwandu, H.E. Sani Abubakar Danladi, Engr Salisu Muhammad Gombe, Ibrahim Baba Suleiman, Alhaji Kawu Adamu Gombe da shugaban JIBWIS Yobe Sheikh Yusuf.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *