Ƴan sanda Sun Kama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Kwanaki 2 Kafin Zaɓen Gwamna

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Edo Jarret Tenebe bisa umarnin mataimakin gwamnan jihar Edo. Hon Philip Shaibu.

An ce an kama Tenebe ne a garinsa na Ikabigbo, karamar hukumar Etsako ta Yamma, saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.

Wannan dai ya zo ne kwanaki biyu kacal a gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a fadin kasar nan.

An tattaro cewa mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Edo, wanda fitaccen mai fafutuka ne ga jam’iyyar APC, kuma mai tsananin biyayya ga tsohon gwamnan jihar Kwamared Adams Oshiomhole, a wani faifan bidiyo na baya-bayan nan ya zargi mataimakin gwamnan da batutuwa daban-daban.

A wani taron manema labarai da ta kira a birnin Benin a ranar Talata, jam’iyyar APC ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta shirya yin magudi a zaben da za a gudanar a ranar Asabar, inda ta yi amfani da wasu ‘yan daba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *