Sojoji Sun Garkame Wasu Gidajen Uwa Ba Kwaba Da Sharholiya A Maiduguri

Gidan Karuwai Maiduguri

Alfijr ta rawaito Dakarun sojin Najeriya sun yi dirar mikiya a gidajen karuwai masu karancin shekaru a Maiduguri da ke Kasuwan Fara, yankin Shagari a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Rufe gidan karuwan ya biyo bayan wani rahoto na musamman da jaridar Daily Trust ta fitar a ranar Asabar da ta gabata inda ta bankado yadda ake tafka ta’asa a gidajen karuwai.

Mazauna yankin da suka tuntubi wakilinmu sun ce an kuma kama wasu mutanen.

“Sojoji sun kai samame wurin kwanaki biyu da suka gabata inda suka kama wasu mutane. Yanzu duk wurin yayi tsit. Ba mu san inda suka kai masu laifin ba,” inji wata mazauni mai suna Halima Abdul.

Ta ce samamen da kuma sintiri da sojoji suka yi a yankin ya canza al’umma zuwa yanayin kwanciyar hankali ga mazauna yankin.

“Mun sha wahala tsawon shekaru na azaba da wahala amma da abin da muke gani a yau, an samu kwanciyar hankali” in ji ta.

Wani mazaunin yankin, Solomon Joseph, ya bayyana samamen a matsayin wani abu mafi kyau da ya faru da al’umma, yayin da ya yi kira ga sojoji da su bar wadanda ke da harkokin kasuwanci su dawo.

“Akwai ‘yan kasuwa da ke gudanar da kasuwancinsu a Kasuwar Fara, muna rokon sojoji da su bar su su dawo dan cigaba da kasuwancin su,” inji shi.

Daga Aminu Bala Madobi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *