Gwamna Abba Ya Ce Dukkanin Kwamishinonin Da Za’a Nada, Su Bayyana Kadarorinsu

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Kano, ya umurci dukkan  kwamishinoni 19 su bi ka’idojin da’ar ma’aikatar da za a kai su

A sanarwar da babban sakataren Yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace, da wannan

Sanarwar tace, ana sa ran wadanda aka zaba za su bayyana kadarorinsu a cikin mafi kyawun lokaci kafin a fara tantance su a majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, 2023 da karfe 10 na safe a harabar majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya sha alwashin cewa babu wani kwamishina da za a rantsar da shi a matsayin memba na majalisar zartaswa ta jihar ba tare da cike fom din bayyana kadarorinsa daga Ofishin hukumar kula da da’ar ma’aikata ba.

“Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi umarnin da aka ba su.”

Gwamna Abba Kabir Yusuf na fatan jaddada aniyarsa ga mutanen jihar Kano cewa gaskiya da rikon amana ya kasance tushen tsarin gwamnatinsa kamar yadda ya sanar tun lokacin kamfen.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Gwamna Abba Ya Ce Dukkanin Kwamishinonin Da Za’a Nada, Su Bayyana Kadarorinsu”

  1. Bayyana kadarori ko rashin yin hakan baya nuna gaskiyar mutum ko akasin haka,tayiwu idan ina cikin waddanda Allah zai bawa kwamishina na ki fadin gaskiyar abin Dana mallaka ,misali ina da Naira dubu goma na iya karawa nace Ina da milliyan dari,kaga anan tunda baza’ace dsni naje na nuna Ina kadarorin nawa suke ba aika ga anyi baya ba zane kenan.
    Abin yi ga mahukunta shine umrce su
    da cewa sun basu Amana Kuma duk Wanda yaci tofa gashi ga hukuncin Allah nan.
    Da Kuma shawarce su da cewa arziki na Allah ne, zallunci bayasa ayi arziki,haka nan adalci acikin shugabanci bayasa ayi arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *