Amurka Tayi Gargaɗi Da Jan Kunne Ga Ƴaƴanta Zuwa Jihohi 18 A Najeriya

Gwamnatin Amurka tana da iyakacin ikon ba da agajin gaggawa ga ‘yan kasar Amurka a yankuna da dama na Najeriya saboda yanayin tsaro.”

Alfijir Labarai ta rawaito ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta shawarci Amurkawa da su kara kulawa yayin balaguron zuwa Najeriya “saboda ayyukan ta’addanci da garkuwa da Mutane da sauran ayyukan ƴan bindiga.”

Bayan sabunta shawarwarin tafiye-tafiyen da aka yi a ranar Laraba, Amurka ta lura cewa wasu yankuna “sun kara zama masu haɗari”

Ta shawarci ‘yan kasarta da su guji zuwa Jihohin Borno Yobe Kogi da kuma arewacin Jihar Adamawa saboda ta’addanci da garkuwa da mutane.

Sanarwar ta kara da Bauchi Gombe Kaduna Kano Katsina Sokoto da Zamfara saboda garkuwa da mutane, sai Abia Anambra Bayelsa Delta Enugu Imo da Ribas (ban da cikin Fatakwal) saboda sace-sacen mutane da gungun yan ta’adda dauke da makamai.

Ya kuma ƙara da cewa “mummunan laifuka – kamar fashi da makami da yin garkuwa da mutane, fashi a gefen hanya da fyade – ya zama ruwan dare a fadin kasar.”

Ya ce, “Satar mutane domin neman kuɗin fansa na faruwa akai-akai, wanda kwanan nan ma ya faru akan wasu ‘yan kasa biyu da suka dawo Najeriya daga ziyara da wani ɗan kasar Amurka mai dukiya, tabbas kungiyoyin ƴan Ta’addan sun kuma addabi al’umma.

‘Yan ta’adda na ci gaba da shirya makarkashiya da kai hare-hare a Najeriya, ‘yan ta’adda na iya kai hari ba tare da wani gargadi ko kaɗan ba a kai a kai, a kan shaguna ko kasuwannin, a otal-otal, ko wuraren cin abinci da cibiyoyin Gwamnati, da cibiyoyin sufuri da sauran wuraren da jama’a ke taruwa.

Ƴan Ta’addan kuma suna aiki ne tare da ɓata garin cikin al’umma don cimma burin su.

Akwai tashin hankalin jama’a da gungun ‘yan bindiga a sassan Kudancin Najeriya musamman a yankin Neja Delta da kuma yankin Kudu maso Gabas, Masu aikata laifuka da suka hada da sace-sacen jama’a da kai hare-hare kan jami’an tsaron Najeriya, su ma sun zama ruwan dare a wannan yanki.

Rikici na iya barkewa tsakanin al’ummomin manoma da makiyaya a yankunan karkara.

Gwamnatin Amurka tana da iyakacin ikon ba da agajin gaggawa ga ‘yan kasar Amurka a yankuna da dama na Najeriya saboda yanayin tsaro.”

Sai dai ta shawarci ‘yan kasar da har yanzu suka zabi tafiya Najeriya da su “Dauki ingantaccen katin shaida gami da fasfo din Amurka tare da bizar Najeriya na yanzu idan ana bukata.

“Kula da kafofin watsa labarai na gida don samun bayanan abubuwan da ke faruwa, kuma ku kasance cikin shiri don daidaita tsare-tsaren ku,
Ku kula da kewayenku, ku
Kasance a faɗake a wuraren da turawan yamma ke yawan zuwa,

Hakazalika a guji zanga-zanga da manyan tarukan siyasa,

Ku yi tsari mai kyau domin ganin ba ku dogara kacokan ga taimakon gwamnatin Amurka ba, Kafa ƙa’idar “tabbacin rayuwa” tare da makusanta ku, domin idan an yi garkuwa da ku ƙaunatattunku su san takamaiman waɗanda aka yi garkuwa da su don tabbatar da cewa kun samu ɗauki a lokacin da ya dace.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *