Babu Gaskiya A Ikirarin Tinubu Na Bawa Jihohi Biliyan 570 – In Ji Gwamna Makinde

Screenshot 20240809 123233 Facebook

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu na cewa gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi 36 Naira Biliyan 570 inda ya ce babu gaskiya a bayanin.

Alfijir labarai ta ruwaito wata sanarwa da Gwamnan ya sanywa hannu kuma aka wallafa ta a shafin gwamnatin jihar a jiya Alhamis, Makinde ya ce kudin da aka bayar ba daga gwamnatin tarayya suke kai tsaye ba.

Gwamnan ya ce kudin da jihohi suka karba, kudin COVID-19 ne daga bankin duniya, inda gwamnatin tarayya ta zama a tsakiya kawai.

Sannan ya ce kudin, an bada su ne domin mayarwa jihohi abinda suka kashe kan cutar COVID-19.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *