Gwamnatin Kano Ta Maka Ganduje Da Garo A Kotu Kan Zargin Karkatar Da Biliyan 57.4

FB IMG 1719477546654

Gwamnatin jihar Kano ta shigar da sabuwar kara na tuhumar tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da Murtala Sule Garo da wasu mutane biyu.

Alfijir labarai ta ruwaito a cewar takardar karar, ana tuhumar Murtala Garo da Lamin Sani da Muhammad Takai da hada kai wajen aikata laifi da zanba cikin aminci da gabatar da bayanan karya da badakalar kudade.

Gwamnatin na zarginsu da wawure kudin kananan hukumomi dake asusun hadaka tsakanin jihar da kananan hukumomi 44.

Sannan ana zargin badakalar kudi ta Naira Biliyan 57.4 da suka karkatar dasu zuwa asusun ajiya na kashin kai.

Haka kuma ana zargin sun sauya kudin zuwa Dalar Amurka.

Haka kuma, gwamnatin na tuhumar su da mallakar kadarori da kudaden a kasar Dubai da Otel a garin Abuja da wasu gidajen mai a Kano.

Gwamnatin dai ta ce zata gabatar da shaidu 143 a gaban kotun a lokacin shari’ar.

NAN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *