Labari Mai Dadi! Kwamatin majalisa ya nemi a rage wa ‘yanmajlisar Najeriya albashi

Majalisa

Kwamatin Majalisar Dattawan Najeriya da ke nazari kan dokar zaɓe ya bayar da shawarar rage albashin ‘yanmajalisa da kuma masu muƙaman gwamnati.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban kwamatin, Sanata Sharafadeen Alli, shi ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin da yake ganawa da ‘yansiyasa da kuma wakilai a ɓangaren shari’a game da aikin kwamatinsa na yi wa dokar zaɓe ta 2022 kwaskwarima, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Najeriya suka ruwaito.

A cewarsa, suna ba da shawarar rage albashin ‘yanmajalisar da kashi 30 cikin 100, yayin da za a rage na masu riƙe da muƙamai da kashi 40 domin rage kashe kuɗin gudanar da gwamnati.

Yayin ganawar, jam’iyyun siyasa sun nemi a dinga gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa, da na ‘yanmajalisar tarayya, da gwamnoni, da ‘yanmajalisar jiha a rana ɗaya, suna masu cewa rarrabawar da ake yi yana jawo kashe kuɗi.

Jam’iyyun sun kuma nemi a haɗa katin zaɓe da lambar ɗan ƙasa ta NIN “domin ƙarin tsaro da kuma rage kashe kuɗi wajen yin rajistar katin zaɓe”.

BBC

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *