Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kwato wasu miliyoyin kudi daga wajen wani mai gadin kamfanin Takalma na Asia Plastic dake unguwar Jogana a karamar hukumar Gezawa dake jahar.
AlfijirLabarai ta ruwaito an kama wanda ake zargin mai suna  Sadam Habu, dan asalin jahar Adamawa, inda ya fasa ofishin mai biyan kudi, bayan ya saci miliyoyin naira a cikin Akwati sannan ya bankawa ofishin wuta.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu labarin faruwar lamarin a ranar 28 ga watan Augustan 2024, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin a lokacin da yake yunkurin tserewa da kudin.
Bayanai sun bayyana cewa kudin da aka samu a cikin akwatin da ya zuba kudin sun haura naira miliyan 20, kuma yanzu haka rundunar ta na ci gaba da gudanar da bincike wanda da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj