Aƙalla sojojin Najeriya 195 sun mika takardun ajiye aiki domin ƙashin kansu ga Rundunar Sojin Najeriya.
Alfijir Labarai ta rawaito sojin Ƙasa ta Najeriya ba ta bayyana dalilin ajiye aikin sojojin ba, amma wasu majiyoyi sun danganta lamarin da rashin ƙwarin gwiwa a tsakanin sojoji, sakamon matsin rayuwa a ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce Babban Hafsan Sojin rundunar ya amince da aniyar sojojin ta barin aiki domin ƙashin kansu.
Nwachukwu ya ce sojojin sun bi ka’ida kuma dokar aikin soji ta tanadi hakan, don haka, za su fara hutun barin aiki daga ranar 1 zuwa 24 ga watan Nuwamba, 2024.
Sanarwar da Birgediya-Janar O.H. Musa ya sanya wa hannu ta ce murabus ɗin sojojin zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan na Nuwamba.
Nwachukwu ya bayyana cewa rundunar ta yanke tattara jerin sojojin 195 da za su bar aiki don ƙashin kansu domin sallamar su a lokaci guda ne saboda ta yi musu kyakkyawan tsari kamar yadda ta saba a tsawon shekaru.
Ya ce hakan ya ba da damar bin dukkan ka’idoji da yin shirye-shiryen biyan su kuɗaɗensu na sallama da kuma fara karɓar fanshonsu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj