Yadda ziyarar Tinubu Ta Kasance Zuwa Maiduguri Domin Ziyarar Jajen Ambaliya

Maiduguri

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Maiduguri na jihar Borno domin jajanta wa al’ummar jihar bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta samu garin.

A jiya ne dai Tinubu ya dawo daga tafiya, inda ya je China da Burtaniya.

Tun ya na can ya umurci mataimakin sa Kashim Shettima da ya ziyarci Maiduguri ya ga abinda ke faruwa.

Sai shi ma Shugaban ya tashi kafa da kafa zuwa Maiduguri, inda ya sauka da misalin ƙarfe 3:20 na rana.

Shugaban ya kewaya guraren da Ibtila’in ya faru tare da jajantawa da nuna alhini kan lamarin

A yayin ziyarar shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin taimakawa waɗanda ambaliyar ta shafa a Maiduguri dake jihar Borno.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *