Daga Aminu Bala Madobi
Makonni kadan gabanin gudanar da zabukan kananan hukumomi a Kano, Shugaban Hukumar KANSIEC Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya yabawa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen kare dimokuradiyya.
Alfijir Labarai ta rawaito yayin wata ziyarar da ya kai ma Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Shiyyar Zone 1 Dake Kano Ari Muhammad Ali, Malumfashi ya jaddada cewa, ‘yan sanda su ne ginshikin tabbatar da doka da oda, da kuma tabbatar da tsaro a harkokin zabe.
Farfesa Malumfashi yayi nuni da cewa aikin ‘yan sanda na da matukar muhimmanci a dukkan tsare tsaren rayuwa ba ga zabe kawai ba, wanda hakan ya sa suka zamo jakadun tabbatar da dimokuradiyya.
“Hakika Kano jiha ce da a ko da yaushe da lamarin ta ke dumama, take daukan zafi, kuma jiha ce da ko yaushe lokacin siyasa ne.” Inji Malumfashi.
Shugaban ya bayyana muhimmancin jihar Kano, kasancewar jihar da ta fi kowacce jiha yawan al’umma, da kananan hukumomi 44, da mazabu 484, da kuma rumfunan zabe 11,222, inda ya jaddada bukatar neman hadin kan ‘yan sanda don bada tsaro mai inganci.
Da yake mayar da jawabi, Mataimakin Sufeton ‘yan sanda shiyya ta 1 Dake Kano AIG Ali Ari, ya bada tabbacin bayar da cikakken goyon baya da hadin kai ga zaben kananan hukumomi da ke tafe, inda ya bada lambar wayar sa domin kira akai rahotanni ga duk wata bukata da ta taso dare da rana.
AIG Ari ya nuna matukar jin dadinsa ga hukumar zaben Kano, inda ya bayyana ziyarar a matsayin ta gwal, kuma irinta ta farko da wani ma’aikacin gwamnati da kai masa “naji dadi wannan ita ce ziyarar farko tun bayan kama aikina da wani ya kawomin” Inji AIG Ali.
Yayin Ziyarar, an gabatarwa da mataimakin sufeton yan sandan ka’idojin zabe da kalandar 2024.
Wannan haɗin gwiwar yana nuna mahimmancin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da hukumomin zabe wajen tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin lumana da nasara.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj