Likitoci a Jihar Kano, sun bayyana damuwarsu kan rashin isassun likitocin da za su ke duba marasa lafiya, wanda hakan ya sa suke shirin tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Alfijir labarai ta rawaito Ęungiyar lkitocin Asibitocin Gwamnati da Likitocin HaĘora ta Ęasa ce, ta bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da sakataren Ęungiyar, Dokta Anas Idris Hassan, ya jagoranta.
Ya ce gwamnatin jihar ta amince a watan Yuni za ta biya musu buĘatunsu, amma har yanzu ba ta Éauki wani mataki ba.
Ęaya daga cikin muhimman batutuwan da suke korafi a kai shi ne rashin biyansu alawus bayan wucewar annobar COVID-19, wanda Gwamnatin Tarayya ta biya tun a 2021, amma Gwamnatin Jihar Kano har yanzu ba ta biya ba.
Dokta Anas ya kuma bayyana cewa likitocin da aka Éauka aiki a watan Satumban 2023 ba su samu albashinsu ba.
Likitocin sun kuma koka kan yanayin asibitocin Kano da rashin manyan kayan aiki. Babbar matsalar ita ce Ęarancin likitocin da za su ke duba marasa lafiya.
A Kano, akwai kimanin mutum miliyan 20, amma likitoci 600 ne kawai suke duba su, wanda hakan ke nufin likita Éaya na kula da marasa lafiya 33,000.
Wannan adadi ya saÉa da Ęaāidar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara.
Saboda waÉannan matsaloli, likitocin suka yanke shawarar tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukanš
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai šš
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj