Katobara: Dubun Wani Matashi Ta Cika Bayan Daya Yi Sata A Wani Gida Ya Kuma Kone Gidan

wuta

An gurfanar da wani matashi a kotu kan sace kayan abinci a wani gida da kuma kone gidan a Jihar Kwara.

Alfijir labarai ta rawaito Hukumar tsaro ta Sibil Difens ta gurfanar da matashin ne kan satar kayan gidan, inda alkali ya tusa ƙayarsa zuwa Gidan Yarin Mandala da ke jihar.

Mai Shari’a na kotun Majistaren ya yanke hukuncin ɗaurin shekara guda ba tare da zaɓin biyan tara ba, bayan da ya samu matashin da laifi.

A ranar 26 ga watan Satumba 2024 ne matashin ya fasa gidan a cikin dare a yankin Onireke, Upper Gaa Akanbi, da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu.

Ya sace kayan abinci da kayan daƙi da sauransu, sannan ya banka wa gidan wuta.

Ya banka wa gidan wuta ne a kokarinsa na tserewa bayan  jama’a sun yi yunkurin kama shi.

Amma daga bisani an yi nasarar kama shi aka damƙa wa jami’an Sibil Difens.

Aminiya

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *