Rundunar tsaro ta farin kaya DSS ta fara binciken Sanata a jihar Bauchi, Shehu Buba, bisa zargin yana da alaka da kasurgumin dan fashin daji, Abubakar Idris.
Alfijir labarai ta rawaito Wata majiya a jihar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa jaridar ThisDay cewa an mika rahoton tsaro kan Sanatan ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Rahotan tsaron, acewar majiyar, an zargi Sanatan mai wakiltar Bauchi ta Kudu da daukar nauyin dan ta’addan zuwa aikin Hajji.
Lamarin, ya sanya jami’an tsaro na DSS kai samame ofishin hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi a yayin aikin Hajjin 2024.
Majiyar ta ce jami’an tsaron sun nemi bayani kan Fasfo din Abubukar Idris da Zainab Aliyu wadanda dukkansu suka yi rijista a matsayin maniyyata a hukumar.
Rahotanni sun ce tun a lokacin DSS suka kama Abubakar Idris acewar wata majiya a hukumar tsaron.
Ana zargin dan ta’addan dai da ayyukan garkuwa da mutane a jihar Zamfara.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj