Rundunar ƴan sandan Jihar Sakkwato ta kama wani matashi mai suna Abba Aliyu kan zargin sa da laifin yin garkuwa da wani ɗan ƙaramin yaro.
Alfijir labarai ta rawaito kakakin rundunar, ASP Ahmed Rufa’i, ya ce sun samu ƙara ne daga wani Ibrahim Shehu a ranar 16 ga watan Oktoba kan cewa ɗansa mai kimanin shekaru biyu ya ɓata tun a ranar 13 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 6 na yamma.
An yi ta ƙoƙarin gano inda yaron ya ke, amma ba ayi nasara ba, har sai da wanda ya yi garkuwa da shi ya nemi a biya Naira miliyan biyu a matsayin kuɗin fansa wanda daga bisani aka biya N500,000 kafin aka sako yaron.
Daga nan ne jami’an suka yi nasarar kama shi bayan gudanar da binciken sirri a yankin Badon Hanya inda nan ne matashin ya ke da zama.
A lokacin da ake gudanar da bincike game da lamarin, matashin ya amsa laifinsa inda ya ce ya yi hakan ne don ya samu kuɗi daga iyayen yaron.
Allah ya kiyashemu taɓawa da aikin da na sani duniya da lahira ameen.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇