Babu wanda ya isa ya hana hukumar zabe gudanar da zaɓen kananan hukumomi – In Ji Gwamna Abba

FB IMG 1723959647845

‘Yan Najeriya musamman mazauna Kano na dakon ganin yadda za ta kaya a gobe Asabar game da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar, yayin da gwamnatin jihar ta kafe cewa sai ta yi shi duk da umarnin kotu da ya ce a dakata.

A ranar Talatar da ta gataba ne wata babbar kotun tarayya a Kano ta rushe shugabancin hukumar zaɓen jihar Kano wato Kano State Independent Electoral Commision (Kansiec) bayan ta gamsu cewa ƴan jam’iyyar NNPP ne.

Mai Shari’a Simon Amobeda ne ya ba da hukuncin bayan wani mai suna Aminu Tiga ya shigar da Kansec da gwamnatin Kano ƙara da wasu 12 ƙara.

Alƙalin ya bayar da umarnin rushe shugabannin hukumar, sannan ta buƙaci a naɗa wasu kafin a gudanar da zaɓen.

Hukunci 10 da kotu ta yanke kan zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano

An samu irin haka a jihar Rivers, inda kotu ta ce a dakata da zaɓen, sannan ta buƙaci jami’an tsaro su guji shiga zaɓen.

Sai gwamnan jihar da hukumar zaɓen jihar suka gudanar da zaɓen, abin ya jawo rikice-rikice kafin da kuma bayan zaɓen – ciki har da musayar yawu tsakanin gwamnan jihar da ƴansanda, wanda ya sa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya saka baki.

Jam’iyyar adawa ta NNPP ce ke mulkin jihar Kano, kuma ita ce kaɗai jihar da jam’iyyar take da kujerar gwamna a ƙasar da ta lashe a zaɓen 2023.

Tuni babbar jam’iyyar adawa a jihar ta APC ta sanar cewa ba za ta shiga zaɓen ba, inda take zargin gwamnatin NNPP da tsawwala kuɗin sayen fom ɗin takara.

Hukumar zaɓe ta Kansec ta sanar da naira miliyan 10 a matsayin kuɗin fom ɗin takara na shugaban ƙaramar hukuma, da kuma miliyan biyar ga duk wanda ke son yin takarar kansila.

Sai labarin yanzu kuma kotu ta yi wa hukumar zaben Kano umarnin gudanar da zaben shugabannin ƙananan hukumomi a jihar kamar yadda suka tsara a baya.

BBC

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *