Jam’iyyar NNPP ta kori Hon Ali Musa Hard Worker daga jam’iyyar

IMG 20241025 WA0304

Daga Rabi’u Usman

Ana tsaka da yanke hukunci a babbar kotun jiha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai Shari’a Usman na Abba a ranar juma a, sai jam’iyyar NNPP ta mazabar Dan Maliki dake Cikin karamar hukumar kumbotso ta fitar da sanarwar ta kori Hon Ali Musa hard worker daga jam’iyyar NNPP.

Alfijir labarai ta rawaito kotun kuma ta tabbatar da Hon Ali Musa Dan Maliki a matsayin halastaccen Dan takarar shugabancin karamar hukumar kumbotso karkashin tutar jam’iyyar NNPP.

Tun a baya dai majiyar mu ta ruwaito cewar, jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya janye sunan Ali Musa hard worker a matsayin Dan takarar shugabancin karamar hukumar kumbotso ya maye gurbin sa da Hon Ghali Basaf a matsayin shi ne wanda zai yiwa jam’iyyar takarar shugabancin karamar hukumar kumbotso karkashin tutar jam’iyyar NNPP.

Inda a wannan rana babbar kotun jiha ta tabbatar da Hon Ali Musa Dan Maliki(Hard worker) a matsayin halastaccen Dan takarar shugabancin karamar hukumar kumbotso karkashin tutar jam’iyyar NNPP.

Yanke hukuncin ya biyo bayan wasu kwararan hujjoji da Lauyan Ali Musa, Barr Jazuli Mustapha ya shigar gaban kotun, inda kuma Lauyan jam’iyyar NNPP da na kansiec suka Gaza bayar da hujja ko guda da zata kalubalanci hujjojin Barr Jazuli Mustapha.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

One Reply to “Jam’iyyar NNPP ta kori Hon Ali Musa Hard Worker daga jam’iyyar”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *