Babbar mai Shari’a ta 9 Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta ce yayin da akwai alkalan kirki da masu karfin gwiwa a bangaren shari’a, wasu tsirarun cikinsu suna bata masu suna.
Alfijir labarai ta rawaito mai Shari’a Kekere-Ekun ta bayyana hakan ne a jiya Asabar yayin wani taron tattaunawa mai taken “Dabi’a, Halayya da Dokar Shari’a,” wanda Kungiyar Kula da Al’adun Musulunci ta shirya don karrama Justice Habeeb Abiru, wanda aka daukaka zuwa Kotun Kolin Najeriya. Ta jinjinawa bangaren shari’ar Najeriya kan jajircewarsu.
Ta jaddada cewa dole ne a dauki ra’ayin talakawa kan yadda dabi’a, halayya da doka ke daidaituwa tare.
Mai Shari’a Kekere-Ekun ta kara da cewa, yadda jama’a ke karbar doka ya danganta ne da yadda ta dace da ka’idojin da suka dace, bukatar bayyana, daidaituwa da ‘yancin bangaren shari’a, da kuma adalcin hukumomin da ke aiwatar da dokokin.
Ta ce, “Matsayin lauya a wannan tsari ya cancanci kulawa ta musamman.
“Lauya, wanda ake kallonsa a matsayin mai jan aiki biyu a fagen shari’a da adalci, dole ne ya tsallaka filin da doka, dabi’a da halayya ke haduwa.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj