Kimanin Mutane 150 Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Ya Musuluntar a Garin TAKAI

IMG 20241202 WA0702

Da yake karanta musu Kalmar Shahada Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci wadanda suka musulunta subi dukkan dokoki da sharrudan addinin musulunci.

Alfijir labarai ta rawaito hakan ya faru ne a wani taron bude Masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyya da Gidauniyar Ganduje Foundation ta Samar a garin Takai dake jihar kano.

Mai Martaba Sarkin ya shaida musu cewa daga lokacin da suka karbi Kalmar Shahada sun zama dai dai suke da kowanne musulmi.

Yace bayan yarda da amincewar da sukayi babu abun bautawa da gaskiya sai Allah guda daya kuma bashi da abokin tarayya, ya zama wajibi su tsayar da Sallah su bada zakka suyi azumi a kowanne wata na Ramadan sannan kuma suje aikin hajji idan Allah ya basu iko.

Daga nan sai Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Gidauniyar ta Ganduje Foundation ta Samar da Malamai wadanda zasu koyar dasu ilimin addinin musulunci domin sanin yadda zasu bautawa Allah madaukakin sarki.

Sarkin ya yabawa kokarin kwamitin Da’awa na Gidauniyar bisa yadda yake kokarin yada addinin musulunci a lungu da sako na jihar nan dama wasu jihohi domin bunkasar addinin musulunci

Inda ya bukacesu dasu cigaba da wannan kokari ladansu naga Allah madaukakin sarki Wanda yayi alkawarin zai bawa duk Wanda ya taimaki addininsa.

Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Babban Sakataren yada Labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *