Yadda Majalisar Wakilai Ta Kaure Da Hayaniya Kan Kudirin Gyaran Haraji.

IMG 20241203 WA2104

Daga Aminu Bala Madobi

A Yau Talata, Zauren Majalisar Wakilai ya runcabe da cece-kuce da fadi-in-fada a lokacin da dan majalisar Wakilai daga jihar Ekiti, Akin Rotimi, ya tabo batun kudirin sake fasalin haraji.

Hayaniyar dai ta fara ne a lokacin da Rotimi, wanda ya tsaya a madadin shugaban kwamitin, Rep. Boma Goodhead, ya yi yunkurin gabatar da rahoto. A yayin jawabinsa, Rotimi ya bayyana cewa: Rahoton ya kasance kan kudirin doka na soke dokar da ta shafi masana’antar mai da iskar gas ta Najeriya ta 2010, da kuma kafa dokar da ta shafi masana’antar mai da iskar gas ta Najeriya.

“Sunana Akin Rotimi Jr. Ina wakiltar al’ummar Ekiti ta arewa, kananan hukumomin Ikole da Oye. Ya mai girma shugaban majalisa, ni dan jihar Ekiti ne, jiha ta farko, wadda ‘yan majalisar wakilan ta na kasa, baki daya suka amince da kudirin dokar haraji,” inji shi.

Wannan tsokaci ya haifar da hayaniya, inda ‘yan majalisar suka yi kakkausar suka na adawa da wannan magana tare da cewa“A’a, A’a, A’a!” Bamaso Bamaso, Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya shiga tsakani, inda ya bayyana cewa kalaman Rotimi na kashin kan sa ne kuma bai kamata a dauke shi da muhimmanci ba.

Shugaban majalisar ya gargade shi da cewa: “Ka Yi jawabin ka kawai kan abinda ya dameka, ba batun haraji ba. Ba magana muke game da kudirin haraji ba, saboda wannan lamari ne mai cike da cece-kuce. A madadin ku, na janye maganar.”

Rotimi ya nemi afuwa tare da janye kalaman nasa, amma ‘yan majalisar ba su gamsu ba. Sun bukaci ya ajiye rahoton gaba daya.

Rotimi ya amince da matsin lamba daga Yan Majalisar, yana mai cewa: “Ina neman izinin Shugaban Majalisa da ‘Yan Majalisa na janye kalamaina na ajiye rahoton.”

Idan za a iya tunawa, A ranar 3 ga watan Oktoba, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi nazari tare da zartar da wasu kudirori guda hudu na sake fasalin haraji na kasa.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *