Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da ajiye aiki da Engr. Muhammad Diggol, yayi a matsayinsa na kwamishinan ma’aikatar bibiyar aiyuka nan take.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikewa da manema labarai
Tun a farkon mulkinsa gwama Abba Kabir Yusuf ya nada Engr. Muhammad Diggol a matsayin kwamishinan sufuri, kafin daga bisani ya saura masa wajen aiki zuwa ma’aikatar bibiyar aiyuka inda a nan ne yayi murabus .
Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Engr. Diggol bisa kokarinsa da jajircewarsa, sadaukarwa, da kuma bin ka’idojin aiki a lokacin da yake zama dan majalisar zartarwa ta jiha.
A cewar sanarwar, Gwamnan ya yiwa Engr. Doggol fatan alheri a harkokin da zai sanya a gaba.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sanya kwamishinan ya ajiye aikinsa ba.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj