Daga Aminu Bala Madobi
An tilastawa jama’a da dama barin gidajensu yayin da rahotanni suka ce ‘yan bindiga sun saka harajin Naira miliyan 173 a kauyuka 25 dake yankin Karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Zagazola Makama, Masanin tsaro cikin wani rahoton binciken yaki da ‘yan tada kayar baya wanda ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ya rawaito cewa, Danisuhu, wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne ke jagorantar ‘yan bindigar.
Rahotonni sun bayyana cewa harajin na kunshe ne da bukatar bada gudumawa ta musamman da suka hada da buhunan wake da kuma barazanar cin zarafi ga wadanda suka kasa biya.
Rahoton ya kara da cewa wadannan bukatu sun tilastawa daruruwan mazauna yankunan yin hijira da gidajensu domin tsira da rayuwarsu.
Makama ya bayyana cewa kauyukan da aka kakabawa harajin sun hada da Gijinzama (N8.5m), Dakolo (N5 miliyan + buhunan wake 20), Gunja (N7 miliyan), Kauyen Kane ( Naira miliyan 5), Kurar Mota (N6 miliyan). Sabon Garin Bakin Gulbi (N2.5 million), Kibari (N3 million), Karda (N5 million), Daga Ciki (N3 million), Biya (N5 million), Barebari (N6 million), Kauyen Magaji (N7 million), Kwaren Maisaje (N10 million), Magazawa (N10 million), Maciya (N5 million), da Unguwar Danhalima (N5 million).
Sauran sun hada da Unguwar Rogo (N5 million), Katanga (N5 million), Magazu (N5 million), Sungawa (N15 million), Rakyabu (N15 million), Yalwa (N2.7 million), Tsageru (N5 million), Gidan Anne (N5 million). Naira miliyan 7), da Kunchin Kalgo (N20 million).
Rahoton ya ce “Daruruwan mazauna wadannan kauyukan sun cika wandon su da iska, suka bar gonakinsu don gudun fargabar tashin hankali saboda rashin biyan makudan kudaden,” in ji rahoton.
“Rashin biyan wadannan kudaden haraji kan haifar da munanan hare-hare daga ‘yan bindigar, inda mazauna yankin ba su da wani zabi illa guduwa,” in ji majiyar.
“Yayin da tsaro ya inganta a kan titin Funtua-Tsafe da kuma cikin garin Tsafe, har yanzu wadannan nasarorin ba su kai ga kauyukan Tsafe ta Yamma ba.”
Rahoton ya kara da cewa mazauna yankin sun bukaci karin jami’an tsaro na dindindin a yankin Tsafe ta yamma, tare da bayar da agajin gaggawa ga mazauna yankin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj