Gwamnan Kano ya rantsar da kwamishinoni 7, da  masu bashi shawara 13, da kuma manyan sakatarorin gwamnati 6

FB IMG 1736171285369

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da karin sabbin kwamishinoni bakwai da  masu bashi shawara na musamman goma sha uku da kuma manyan sakatarorin gwamnati guda shida.

Da yake rantsar da sabbin kwamishinonin a gidan gwamnati, gwamna Abba ya hore su su zamo masu gaskiya da rikon amana a yayin gudanar da ayyukansu.

Sabbin kwamishinonin da gwamnan ya rantsar sun hada da Alhaji Shehu Wada Shagagi – Ma’aikatar kasuwanci da masana’antu, sai Ismail Aliyu – ma’aikatar kudi, da Alhaji Gaddafi  Shehu ma’aikatar lantarki.

Sauran sune Alhaji Dahiru Hashim ma’aikatar Mahalli, da Abdulkadir Abdulsalam ma’aikatar Raya karkara da cigaban al’umma, da Kwamred Ibrahim Waiya ma’aikatar yada labarai, da kuma Alhaji Nura Iro Ma’aji ma’aikatar kula da kadarorin gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace nadin nasu an yi shi ne bisa cancanta la’akari da kwazonsu da gudummawar da suke bayarwa wajen cigaban al’umar jihar Kano.

Kazalika gwamnan ya sauyawa Adamu Aliyu Kibiya daga ma’aikatar kasuwanci zuwa ma’aikatar Jin Kai.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *