Daga Aminu Bala Madobi
Ministan Harkokin Bada Agajin gaggawa da Rage Radadin Talauci, Nentawe Yilwatda, ya ce wasu ‘yan siyasa na kokarin yin tasiri kan talakawa ‘yan Najeriya kan tsarin musayar kudi na kai tsaye don jin dadin kudaden da gwamnati za ta rabawa talakawa.
Minista ya yi wannan zargin a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin.
Yilwatda ya ce wadannan ’yan siyasa suna yunkurin karkatar da hankulan mutane masu karamin karfi da aka sanya sunayen su cikin tsarin baiwa mara sa karfi tallafin kudade, da nufin cin gajiyar shirin mika kudi na gwamnati gare su.
Saidai ministan bai bayyana yan siyasar dake kokarin Maida hannun agogo baya ba.
A cewarsa, yayin da yake akwai ‘yan Najeriya miliyan 19.8 da suka yi rajista a cikin shirin zamantakewar, gwamnati ta tabbatar da sunayen mutane miliyan 1.2 kacal.
“Wasu mutane suna son mu karkatar da sunayen mu baiwa gwamnoni ko jihohi su fitar da jerin sunayen kawai su aika”in ji Ministan a wani taron manema labarai.
“Don haka, ba za mu yi la’akari da barin duk wata alaƙa ta siyasa ko abin da zai kawo tasgaro a aikin mu ba. Talauci bai san jam’iyyar siyasa ba, talauci bai san kabila ba. Talakawa talaka ne gaban mu.”
Ya ce shirin za ayi shi ne a bayyane a fili, kuma a wannan karon, za su ci gaba da tafiyar da kingiyoyin al’umma CSOs ta yadda duk abin da za a biya, za su nemi su tantance tare da bin diddigin abin da ma’aikatar ke da shi.
A cewarsa, akwai bukatar ma’aikatar ta tantance dukkanin rajistar ta yadda za a iya tantance ainihin mutanen da ya kamata su ci gajiyar, da tantance wuraren da suke, da gidajensu, da inda suke, da kuma daukar bayanan wuraren dasuke zaune.
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kammala shirye-shiryen sake fara musayar tura kudaden kai tsaye ga talakawa da marasa galihu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ