Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ƙaryata rahoton dake cewa ya soke yarjejeniyar hidimomin alhazai da wasu kamfanoni na Saudi Arebiya domin aikin Hajjin bana.
Rahotanni sun bayyana cewa Ƙungiyar shugabannin hukumomin jin daɗin Alhazai ta Jihohi ta zargi Shugaban na NAHCON da soke kwangilar wani kamfani da ke Saudiyya kai tsaye, wanda hakan na iya kawo cikas ga Hajjin 2025.
Ƙungiyar, ta bakin Sakatarenta, Alhaji Abubakar Salihu, wanda shi ne Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Adamawa, ta yi gargadin cewa soke yarjejeniyar da aka yi da kamfanin Mashariq Al-Dhahabiah na Saudiyya na iya hana Alhazan Najeriya samun takardun izinin shiga Saudiyya don Hajjin 2025.
Sai dai bangaren shugaban na NAHCON ya musanta zargin, a martanin da masu yada labarai na hukumar NAHCON suka fitar.
A cewarsu, zargin bai da tushe balle makama, kuma an yi hakan ne don kawo cikas ga shirye shiryen aikin Hajjin na Bana.
Shi ma a nasa martanin, Shugaban na NAHCON ya bayyana cewa: “Gwamnatin Saudiyya ce da kanta ta soke kwangilar a karon farko, daga bisani ta sake amincewa da ita sannan ta sake soke ta karo na biyu. Don haka, babu hannunsa a cikin soke yarjejeniyar.
“Saboda wannan matsala, na zo Saudiyya don tabbatar da an yi abin da ya dace bisa doka da gaskiya, kuma ina tabbatar muku cewa babu Alhaji da zai rasa damar zuwa Hajjin bana.” In ji shi.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ