Daga Aminu Bala Madobi
Tsohon Gwamnan Osun Alhaji Rauf Aregbesola ya gabatar da wani kwarya kwaryan taro da Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP Sanata Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso A Lagas.
Rahotonni sun ce taron ya gudana ne a gidan Tsohon Gwamnan Aregbesola Dake Lagas kwanaki kadan bayan da Jam’iyyar APC ta kore sa Daga Jam’iyyar.
A wani rubutu, Da Sanata kwnkwaso ya wallafa a shafin sa na X yace “Mun tattauna muhimman abubuwa na cigaban kasa dakuma lissafin Siyasa don ceton kasa” Inji kwankwaso.
Aregbesola Wanda yayi Gwamna karo biyu a jihar Osun, a Jam’iyyar APC an Kore sa Daga Jam’iyyar bisa zargin yiwa Jam’iyyar zagon kasa.
Gboyega Oyetola dai shine Wanda ya gaji Aregbesola bayan kammala wa’adin mulkinsa a jihar Osun.
Sanarwar tace “A bayan taron koli mun yanke shawarar korar Aregbesola Daga Jam’iyyar bisa zargin lefin cin amana”
Ko me kuke tunani gameda wadannan siddabarun siyasa gabanin kakar zaben 2027!?
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ