Daga A’isha Salisu Ishaq
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta na yin duk mai yiwuwa domin magance Siyasar cin mutuncin mutane musamman a gidajen Radio dake jihar.
” Tabbas Gwamnan Kano ya damu matuka da wannan abun da ya ke faruwa a Kano, kuma ya dora mana alhakin kawo gyara don ganin ana gudanar da harkokin Siyasa a Kano ba tare da cin zarafi ba”.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki a sha’anin yada labarai, wanda hukumar kula da kafafen radio da talabijin ta kasa NBC ta shirya a Kano.
Ya ce a kokarinsa na ganin ya magance matsalolin cin zarafin al’umma a kafafen yada labaran musamman Radio, Kwamared Ibrahim Waiya ya ce ya zauna da sojojin baka kuma ya fada musu kudirin gwamnatin Kano, sannna an kafa musu kungiya ta “Gauta Club” domin sanin su waye su ke magana a gidajen Radio da kuma samun bayanan su.
” Tuni mun sanya su na yin rijistar ya’yan kungiyar kuma daga haka ne gwamnatin Kano za ta sami bayanansu da kuma sanin yadda za ta magance matsalar, domin ba za ka iya magance matsala ba idan ba ka santa ko ka san wanda yake aikatata ba” . Kwamishina Waiya
Ya ce akwai bukatar al’ummar jihar Kano su tashi tsaye domin tallafawa kokarin gwamnatin jihar Kano wajen magance wannan matsala, ta hanyar kyamatar masu cin zarafi al’umma da sunan yankin fadin albarkacin baki.
Ya kuma hori masu gabatar da Shirye-Shiryen Siyasa a gidajen Radio a Kano da su ba da tasu gudunmawar ta hanyar daina ba da damar cin zarafin al’umma.
” Abun mamaki a Kano ne za ka ji mutam yana cin zarafin sarki ko gwamna kawai saboda ya nada Naira dubu 10 , kuma ka ga yana yawo abunsa ba tare da an dauki wani mataki akansa , tabbatas gwamnatin Kano ba zata lamunci wannan dabi’ar ba.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD