Majalisar Dattawa data wakilai sun goyi bayan matakin sanya dokar-ta-ɓaci da Tinubu ya yi a jihar Rivers

FB IMG 1742494211343

A majalisar dattijai shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya karanta wasikar shugaban ƙasa da neman amincewar majalisar kan dokar-ta-ɓacin.

Daga nan ne sai majalisar ta shiga ganawar gaggawa na sirri.

Bayan an fito daga ganawar ne sai Akpabio ya sanar da matakin tare da bada damar zaɓe na baki, inda sanatocin da su ka zaɓi a sanya dokar-tabacin su ka samu rinjaye.

Hakazalika takwararta ta majalisar Wakilai ta kada kuri’a da rinjaye domin goyon bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.

Wannan ya biyo bayan wasikar da Shugaba Bola Tinubu ya aiko wa Majalisar Wakilai, inda ya nemi amincewarta kan ayyana dokar ta-baci a wannan jiha da ke yankin Kudu maso Kudu.

Majalisar ta kada kuri’a don goyon bayan wannan mataki yayin zamanta na ranar Alhamis. A cewar Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbass, ‘yan majalisa 240 ne suka halarci zaman, wanda ke nufin an samu kason da ake bukata don yanke shawara.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *