Daga Aminu Bala Madobi
Mataimakin Kwanturola mai kula da Cibiya Da Gidajen Horas da Kangararru Dake Billiri (MSCC) ya karbi bakuncin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kano Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya, Wanda ya kai ziyarar gani da ido tareda yiwa fursunonin tagomashin muhimman kayayyaki.
A yayin ziyarar ta sa, malamin mai fafutukar kare hakkin bil’adama, ya yi nasiha tareda yiwa fursunonin wa’azi a cikin farfajiyar gidan, inda ya jaddada muhimmancin zama ‘yan kasa masu kishi da bin doka da oda da kuma kauracewa aikata laifuka idan aka sake su.
Tun da farko a jawaban da ya gabatar, Mataimakin Kwanturola na gidajen gyaran halin ya nuna jin dadinsa bisa ziyara ta musamman da malamin ya yi.
“Babu shakka munji dadi bisa wannan ziyara mai cikeda tarihin da fitaccen malamin ya kawo wannan gida ta hanyar yi musu waazi tareda jan hankalin su gameda kauracewa aikata laifuka”
Mista Yunana Musa ya bayyana shirin sa na samar da cibiyoyin koyon sana’o’i a cikin gidaje da cibiyoyin gyaran halin da ake tsare da su, da nufin ci gaba da shagaltar da fursunonin a lokacin da ake tsare su.
Mista Musa ta yi godewa mashahurin malamin bisa bayar da gudummawar kayan masarufi da suka hada da kayan abinci, kayan yaji, kayan wanki, sabulu, da tufafi ga fursunonin.
Wannan mataki da abin karimci na alheri na nuna irin himmar da malamin yake da shi wajen kyautata jin daÉ—i da kuma gyara halayen fursunonin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD