Atiku ya tabbatar da haɗakar ‘yan adawa don kawar da Tinubu a shekarar 2027

FB IMG 1742494883002

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya tabbatar da kafa wata haɗakar ‘yan adawa da nufin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, 20 ga Maris, 2025, a Cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja.

Taron ya haɗa manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki a siyasar Najeriya, inda suka tattauna batun ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas kwanaki biyu da suka gabata.

Da aka tambaye shi ko wannan haɗaka za ta zama babbar ƙungiyar adawa a zaɓe mai zuwa, Atiku ya amsa a taƙaice da cewa, “Eh.”

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *