Innalillah wa Inna Ilaihi Raji’un. Allah ya yiwa mahaifiyar Gwamnan Katsina rasuwa

FB IMG 1742734169156

Allah ya yi wa mahaifiyar gwamnan jihar Katsina Dikko Radda Hajiya Safara’u Umar Baribari rasuwa bayan fama da doguwar jinya.

Daraktan yada labaran fadar gwamnatin Jihar Katsina  Ibrahim Kaula Mohammed ne ya tabbatar da rasuwar cikin sanarwar da ya sanya wa hannu a yau lahadi.

Sanarwar  ta ce za a yi jana’izar marigayiyar da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Lahadi a garin Radda.

Daga cikin ‘ya’yan da ta bari akwai mai garin Radda Kabir Umar Radda, da Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar tsohon shugaban Najeriya marigayi Umar Musa Yar’adua.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *