Allah ya yi wa mahaifiyar gwamnan jihar Katsina Dikko Radda Hajiya Safara’u Umar Baribari rasuwa bayan fama da doguwar jinya.
Daraktan yada labaran fadar gwamnatin Jihar Katsina Ibrahim Kaula Mohammed ne ya tabbatar da rasuwar cikin sanarwar da ya sanya wa hannu a yau lahadi.
Sanarwar ta ce za a yi jana’izar marigayiyar da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Lahadi a garin Radda.
Daga cikin ‘ya’yan da ta bari akwai mai garin Radda Kabir Umar Radda, da Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar tsohon shugaban Najeriya marigayi Umar Musa Yar’adua.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD